✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kulob din Plateau United ya cancanci ya lashe kofin firimiya na bana – Golbe

Kyaftin din kulob din Plateau United, Elisha Golbe ya bayyana jin dadinsa kan yadda suka samu nasarar lashe kofin gasar premier ta Najeriya (NPFL), sannan…

Kyaftin din kulob din Plateau United, Elisha Golbe ya bayyana jin dadinsa kan yadda suka samu nasarar lashe kofin gasar premier ta Najeriya (NPFL), sannan ya jaddada cewa idan har akwai kulob din da ya dace ya lashe kofin gasar to babu sama da kulob dinsa.

Kyaftin din ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya bayan an kammala wasan karshe na gasar premier tsakanin kulob dinsa da kuma Enugu Rangers a filin wasa na Rwang Pam da ke Jos a ranar Asabar din da ta gabata.

Kulob din Plateau United ya samu nasarar doke kulob din Rangers da ci 2-0 ta hannun Emeka Umeh da Benjamin Turba, inda hakan ya sanya ya samu nasarar lashe kofin a karo na farko a tarihin gasar. Kulob din Plateau United ya samu maki 66 daga wasanni 38, inda ya bada tazarar maki hudu ga kulob din da ke bi masa baya, wato Mountain of Fire Ministries bayan ya samu rashin nasara da ci 2-1 a hannun kulob din Elkanemi Warriors a garin Maiduguri.

Kyaftin din wanda dan wasan baya ne ya ce sun samu nasarar lashe kofin ne sakamakon jajircewar da suka da kuma hadin kansu da nuna kwazo da kuma bin umarnin da mai horarwarsu Kennedy Boboye ya ba su.

Ya ce, abu ne mai dadi da nishadi mutum ya kasance gwarzo, don haka lashe kofin ya sanya suna cikin wani yanayi na farin ciki da har ya mutu ba zai taba mantawa da wannan ranar ba.

Ya ce, “Na san za ku shaida cewa mun shafe fiye da kwana 200 muna jagorancin gasar, mun ci kwallaye 49, sannan an ci mu 25, inda muke da rarar kwallaye 24, babu kulob din da ya yi abin da muka yi a gasar a bana, ka ga kuwa idan haka ne babu kulob din da ya cancanta ya lashe kofin gasar idan ba mu ba, kuma hakan ya nuna da guminmu muka ci. Abin alfahari ne mutum ya kasance gwarzo ko ya kasance na daya a jerin gasa.”

 “Mun samu nasara sakamakon hada kanmu wuri daya, mun kuma jajirce hade da nuna kwazo da kuma sadaukar da kai kan abin da muke nema, ba a bagas muka ci kofin ba.” In ji shi.

Golbe wanda yake da hannu a kwallaye 11 daga cikin 49 da kulob dinsa ya ci a gasar bayan ya ci kwallaye biyar, ya kuma taimaka aka ci kwallaye shida, ya gode wa Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong bisa ga gudunmuwar da ya ba su, sannan ya gode wa hukumar gudanarwar kulob dinsa da kuma magoya bayansu kan rawar da suka taka har kulob din ya samu wannan gagarumar nasarar.