Kulob din Enyimba na garin Aba ya sake kafa tarihi saboda ya lallasa kulob din Warri Wolbes inda ya lashe kofin da ake yi wa lakabi da kofin tarayya wanda a da ake kira Challenge Cup.
Kulob din Enyimba wanda ya lashe kofin har sau uku ya lallasa na Warri Wolbes da ci 5 da 4 a bugun daga- kai- sai- mai- tsaron- gida (fanariti) a wasan da aka gudanar a filin wasa na Teslim Balogun da ke unguwar Surulere da ke Jihar Legas a karshen makon da ya gabata.
Kulob din Warri Wolbes ne ya fara zura kwallo a ragar na Enymba inda dan wasa Najare Musa ya zura kwallon  Dukkanin bangarorin biyu sun tafka kura-kurai da asarar cin kwallo a lokuta daban-daban kafin hutun rabin lokaci.
dan wasa Bright Esieme shi ne ya farke cin da Warri Wolbes ta yi wa Enyimba bayan minti 65 da fara wasa.
Kulob din Warri wanda ya rika yin wasan kare gida ya samu nasarar cin kwallo ta biyu a lokacin da dan wasan kulob din mai suna Osadiaye Joseph ya zura kwallo a ragar Enyimba a minti na 76 da fara wasa.
Murna ta komawa kulob din Warri Wolbes ciki ne a lokacin da dan wasan Enyimba Uwadiegwu Ugwu ya zura kwallo a ragar Warri Wolbes wanda hakan ya sanya su kaiwa ga bugun daga- kai- sai- mai- tsaron- gida.
A bugun daga- kai- sai- mai- tsaron- gida ne kulob din Enyimba ya samu nasarar cin kwallo biyar sannan a hnnu daya kulob din Warri Wolbes ya zura kwallo hudu ya zubar da daya wanda hakan ya ba Enyimba nasara.
Kulob din Enyimba ya sake kafa tarihi na lashe kofin kalubale na kasa
Kulob din Enyimba na garin Aba ya sake kafa tarihi saboda ya lallasa kulob din Warri Wolbes inda ya lashe kofin da ake yi wa…