✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kulob da dama sun fara rububi a kan golan Najeriya

Rahotannin da kafar watsa labarin wasanni ta SuperSport ta kalato a ranar Talatar da ta wuce sun nuna kulob da dama ne daga kasashen Faransa…

Rahotannin da kafar watsa labarin wasanni ta SuperSport ta kalato a ranar Talatar da ta wuce sun nuna kulob da dama ne daga kasashen Faransa da Afirka ta Kudu da Masar da Tunisiya da kuma Isra’ila  suke rububi a kan golan Najeriya Ikechukwu Ezenwa.

Kamar yadda rahoton ya nuna, kulob din sun fara zawarcinsa ne saboda namijin kokarin da ya yi a Gasar Cin Kofin Afirka ta ’yan kwallon gida (CHAN) da gasar cin kofin WAFU da kuma a Gasar Neman Hayewa Cin Kofin Duniya.

Kamar yadda Emmanuel, Shugaban Kamfanin Gzedsports Management Company na Afirka ta Kudu da ke dillancin ’yan kwallo ya nuna, ya ce yanzu haka kulob da dama ne suke zawarcin dan kwallon kuma akwai yiwuwar nan gaba kadan ne zai rattaba wa daya daga cikinsu hannu in sun kulla yarjejeniya.

Shi dai Ezenwa da yanzu haka yake yi wa kulob din IfeanyiUbah kwallo, tauraruwarsa ta haskaka ne musamman a wasannin da ya kamawa wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da hakan ta sa sunansa ya daukaka.