✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kullum sai na saurari karatun Pantami —Sarkin Kano

Mai Martaba Sarkin sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce rana ba ta fitowa ta fadi ba tare da ya saurari karatun Sheikh Ali…

Mai Martaba Sarkin sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce rana ba ta fitowa ta fadi ba tare da ya saurari karatun Sheikh Ali Isa Pantami ba.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana haka ne a wajen taron kadamar da littafin da mai bawa Tsohon Gwmnanan Jihar Kano shawara a fannin yada labarai, Dr Sule Ya’u Sule ya wallafa.

Littafin mai lakabin “An Introduction to Strategic Communication” an kaddamar da shi ne a Nicon Luxuary Hotel da ke Abuja a ranar Alhamis.

Sarkin Kano, wanda shi ne uban taron ya ce, “Na saurari bayanai daga wuraren mutanan da nake girmamawa.

“Na farko dai akwai shugaban wannan taro, Sheikh Pantami; Kullum idan na hadu da shi ina fada wa mutane yana daya daga cikin malaman da muke girmamawa a wannan kasar.

“Kuma duk da ban zauna a gabansa na dauki karatu ba, amma ina kiran sa malamina, domin babu yadda rana za ta fito ta fadi ban saurari wani abu daga gare shi ba a kan waya.

“Muna godewa Ubangiji da wannan ni’ima da ya yi mana.

“Na biyu shi ne Sardaunann Kano. Dukkaninku kun san alakarsa da mahaifinmu. Sun yi zaman lafiya da girmamawa.”