A tsakanin ranakun sili da babban lauje zuwa sili da manuniyar saman watan Marisa, na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, na yi balaguro zuwa kasar Niyar Jari, inda na kai ziyara garin Tenhiya. Kuma a makon da na sauka a Tenhiya aka yi bikin nadin babban mutum mai rawani, Ahmad Aghali Ibba, wanda ya bayyana wa mahalarta bikin wankan sarautarsa ‘Kukan Tenhiya,” al’amarin da ya ce kofar hanci ne.
Hakika duk Bahaurobiyen da ke bukatar kai ziyara garin Tenhiya, tabbas zai ci kwakwa, domin babu kwalta a titin zuwa garin. Sannan sai mutum ya cilla ya nufi hanyar zuwa birnin Tagadas; da ya iso birnin Tanout, sai ya tsahirta, don sauya akalar tafiya, inda zai yanki daji ya yi ta lulawa a cikin rairayin Hamada, har na tsawon sa’o’i tsayuwa bisa kafa daya. daukacin fadin Tenhiya kwakware karamin lauje ake amfani da su don kwankwadar na-kwadi; mashayar Fura-mai-kyau ga ’yan dugwi-dugwi sili ce, amma duk da haka al’ummar wannan gari na cikin walwala da annashuwa.
Garin Tenhiya na da arzikin amale, domin har wata magana suke fada cewa ‘duk wanda bai mallaki amale babban lauje da zagaye ba, to me zai zauna ya yi a cikin daji?’ Batu na ingarman karfen karafa, Tenhiya na da yawan bisashe duk da kasancewarta a cikin tsakiyar Hamada. Kuma a garin Tenhiya ba a amfani da kurtun magana na halo-alalo, sannan babu gidan Bokan Turai, amma duk da haka mutane ne masu shirya ruguntsimin biki, su yi ta rera wakoki da kidin jita.
’Yan makaranta, masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a Farfajiyar Dodorido da ke Amintattar Jaridar kasar Haurobiya, ba don gudun kada a ce Malam ya rausaya ba, musamman a lokacin da wata mai alfarma ke karatowa da na ba ku labarin kayataccen bikin da aka gudanar a Tenhiya, don murnar samun babban mutum mai rawani a kan karaga, wanda zai ci gaba da jan ragamar al’ummar garin iyakar zamaninsa.
Babban darasin da nike son bijiro wa Haurobiyawa game da garin Tenhiya, shi ne, gari ne mai dadin rayuwa ga wanda ya saba, sannan ga wanda bai saba ba kuwa, zai yi matukar jigata.
Bayan an kammala ruguntsimin bikin wankan mukamin babban mutum mai rawani na garin Tenhiya, sai aka tayar da Shugaban Abzinawan Tenhiya, Ahmad Aghali don ya yi jawabi ga manyan baki. Da ya samu ya tsaya kyam, sai ya yi rabon amale ga Gwamnan Zinder da babban Mutum Mai Rawani na Damagaran, sai kuma ya bijiro da kukan al’ummarsa, inda ya bukaci wadannan gunduma-gunduman baki da su isar da sakonsa ga Shugaba Muhammadou Issoufou. “Kukan Tenhiya kofar hanci ne: Satar bisashe ta yi mana yawa, mun san ba za a iya hanawa ba, amma a rage. Babu likon alakar sadarwar kurtun magana a Fartago; Tenhiya mutane suna da yawa, amma babu wurin likita, idan mai juna karamin lauje za ta zazzago jinjiri ko jinjinniya, sai an sha wahala,” inji shi.
Al’amarin Ahmad Aghali ya yi matukar burge ni, domin yana da masaniya kan abin da ke ci wa al’ummarsa tuwo a kwarya, watakila shi ya sa bai tsaya yi wa manyan mutane surutu rututu ba, tamkar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, nan da nan ya bayyana kukansu. Ni kuwa da an kyale ni, sai in ce, tsananin wahalar da ake sha wajen tafiya Tenhiya, ai kawai sai a sauya wa garin suna zuwa “Tunanin Hanya.”
Abin tambaya a nan shi ne, shin shagabannin Haurobiyawa sun san kukan al’ummarsu, ballantana su bijiro da shi, ta yadda za a lalubo bakin zare wajen yi wa tufkar hanci? Wannan na nuni da cewa Ahmad Aghali na da tunanin al’ummarsa, musamman kan yadda zai samar wa Abzinawa maslahar rayuwa, ta yadda za su samu walwala.
Mu kuwa a kasar Haurobiya, lokacin da aka nada Mai martaba Babban Mutum Mai rawani na Birnin Dabo, wato Masanin Sisi-da-sisi, sai kawai mukarraban jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta bai wa shugaban kasar Haurobiya shawarar daukar nauyin wadanda za su tayar da yamutsi a wannan birnin mai tsohon tarihi. Da Maiduka ya tarfa wa garin mutanen birnin Dabo nono, sai kawai Gwamna Mai Kwarankwatsin-tsiya ya jajirce wajen ganin ya tabbatar da Masanin Sisi-da-sisi a kan karaga; kuma daga bisani wadanda aka jinka wa ’yan matsabbai don su tayar da kayar baya, sai suka rika tona asirin kansu, har ta kai ga wasu sun furta cewa mun cake Hauronmu, amma ba mu yi hargitsi ba.
A ture batun waskiya, Masanin Sisi-da-sisi ina da tabbacin cewa ya san kukan mutanen birnin Dabo, tamkar yadda Aghali ya san kukan mutanen Tenhiya. Don haka a matsayina na Babban Direban Alli, a wannan farfajiya, ina ganin akwai bukatar Masanin Sisi-da-sisi ya yi amfani da kwarewarsa, wajen share wa Arewatawa hawayensu; kuma ya rungumi ’ya’ya da mukarraban Marigayi Babban Mutum Mai rawani, wanda ya kwanta dama a makonnin da suka arce. Uwa-uba, kada Mai martaba ya sake ya shiga harkar Dama-dama da kurda-kurdar wasan Samson Siya-siya, ta yadda zai kauce wa shiga gungun masu yi wa al’umma Damo-da-kura-da-diya.
Mai martaba Masanin Sisi-da-sisi kukan Kanawa malala gashin tunkiya ne, don haka sai ka zakulo muhimmai don tunkararsu. Lallai a daidaita tsarin koyon watsattsaken kolon Malam da Gardi, ta yadda za a hana su laluben dan kanzo da gararambar ‘Maula ta sidi, maula ta Balarabe.’ Ka yi fafutikar tabbatar da adala, ka kuma kawar da juhala. Magajin Dabo, sai ka san kukan al’umma za mu tabbatar ka gaji Abbas. Muna rokon Maiduka ya taya ka riko. ’Yan makaranta ku ce amin!
Kukan Tenhiya
A tsakanin ranakun sili da babban lauje zuwa sili da manuniyar saman watan Marisa, na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa…