✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kudin Banufe

Wani Banufe ne yana cikin tafiya sai ’yan fashi suka tare shi, ya ruga a guje, suka bi shi suka kamo shi da kyar. Sai…

Wani Banufe ne yana cikin tafiya sai ’yan fashi suka tare shi, ya ruga a guje, suka bi shi suka kamo shi da kyar. Sai babbansu ya ce su caje shi su kwashe duk abin da ke aljihunsa. Koda suka lalube dukkan aljihunansa ba su sami komai ba sai Naira 200. Babbansu ya ce: “Tir da kai Banufe, kai da don 200 kake gudunmu?” Sai Banufe ya ce: “Ai na zata kudin albashina ne da na boye a cikin takalmana za ku kwace mani, shi ya sa na ruga.”
Daga Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi 08095968366