✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kudancin Kaduna: An kaddamar da shirin zaman lafiya

Kwamitin zaman lafiya zai kawo karshen tashe-tashen hankula a Kudancin Kaduna

Alummomi a Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna sun kaddamar da shirin zaman lafiya da nufin kawo karshen rikice-rikice a yankin.

Shirin zaman lafiyan wanda Agwatyap, Dominic Yahaya, ke jagoranta ya kunshi kwamitin tsaro da zaman lafiya mai mutum 80 da aka zabo daga kabilun karamar hukumar ta Zangon Kataf.

’Yan kwamitin sun fito ne daga kabilun Kataf, Hausawa, Fulani da kuma Igbo.

Sun kuma hada da Musulmi da Kiristoci da matasa da mata da wakilan kungiyar Miyetti Allah da na kungiyoyin fararen hula.

Basaraken ya ce an kafa kwamitin ne bayan kulla yarjejeniyar bayan taron ranar 22 ga watan Agusta, wanda ya kai ga samun zaman lafiya a yankin.

Basaraken ya ce domin wanzar zaman lafiya a yankin, wajibi ne a aiwatar da dukkannin yarjeniyoyin da aka kulla bayan taron na zaman lafiyar da aka yi.

Ya ce da hakan ne yarjeniyoyin za su yi aiki a daukacin lunguna da sako da ke karamar hukumar, wanda ya ce shi ne makasudin kafa kwamitin na tsaro da zaman lafiya a yankin.