Dan takarar Majalisar Wakilai a mazabar Katsina daga Jihar Katsina, Dokta Lawal Bala Sulaiman, ya ce kudaden da daliget ke karba domin zaben ’yan takara za su iya kai su wuta.
Ya yi kira ga wakilan jam’iyyar da ke da alhakin tantance ’yan takara a matakin kasa da jiha da kuma kananan hukumomi da su guji karbar cin hanci daga hannun masu neman takara a duk wata kujera ta siyasa a yayin zaben fidda gwani.
- Hayatu-deen ya fasa neman takarar shugaban kasa a PDP
- Bayan shan kaye, Sanata ya sa deliget su dawo da motocin da ya ba su
- APC ta dage taronta na zaben dan takarar shugaban kasa
“Matukar dai zukatan daliget sun mutu, suka aikata irin wannan danyen aikin, to hakika tamkar sayar da ’yanci da mutuncin talakawa ne wadanda su ne suka turo su a matsayin wakilai domin su wakilce su a zaben fidda gwani,”in ji shi.
Dokta Lawal Balas ya ce bai kamata hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su EFCC da ICPC su bari a rika yin irin wannan badakala ba, wanda ya jefa Najeriya cikin talauci da rashin tsaro.
Ya kuma ce kawar da cin hanci da rashawa ita ce hanya daya tilo da ke canza kyawawan dabi’un al’umma zuwa ‘ina banza’.
“Matukar daliget ba su daina siyar da ’yancin talakawan da suke wakilta ba, a hankali shugabanci zai ci gaba da tabarbarewa ta yadda miyagun ’yan siyasa za su yi amfani da kudadensu su kai wani matsayin da za su kara daukaka a cikin munanan ayyukansu, kuma su zama annoba mafi girma a cikin al’umma.” In ji shi.
Aminiya ta ruwaito cewa Dakta Lawal Bala Sulaiman ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu, 2022 a Katsina.
A lokacin taron dan siyasar ya gargadi mutane da kada su yarda da duk wani dan takarar da ya bai wa daliget kudi su zabe shi kuma ya ci zaben fidda gwani.
A cewarsa, idan har dan takara ya ci zaben fidda gwani saboda kudaden da ya bai wa daliget, to wannan alama ce da ke nuna cewa dan takarar ba mutumin kirki ba ne.
Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkokin shari’a da su sanya ido wajen tunkarar wannan lamari tare da hukunta duk wanda aka samu da aikata wannan danyen aiki wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya da na jam’iyyar APC.