Cibiyar Nazarin Ayyukan Majalisa da Dimokuradiyya ta Najeriya (NILDS) ta bukaci a kara kudaden da ake ware wa ’yan majalisa domin ayyukan sa’ido ga bangaren zartarwa.
Shugaban cibiyar, Farfesa Abubakar Sulaiman ne ya yi kiran a ranar Juma’a lokacin da ya karbi bakuncin Kungiyar Wakilan Kafafen Yada Labarai na shiyyar Abuja.
- An lakada wa Fasto da ɗan cocinsa duka kan zargin satar mazakuta
- Abin Da Ya Kamata A Yi In Ana Son Hana ‘Yan Najeriya Zuwa Ci-Rani A Turai
Ya ce ’yan majalisar na fuskantar tarin kalubale a yunkurinsu bin diddigin yadda bangaren zartarwa ke ayyukansa ba tare da wata fargaba ba.
Ya ce, “Na sha fada cewa batun duba ayyuka ma cike da tarin kalubale da dole sai an dada samar da kudaden yin hakan, na yi amannar kuma wannan shi ne abin da ’yan Najeriya ke son ji.
“Yanzu alal misali, idan ’yan majalisa za su je duba duba ayyukan hukumomi irin su NPA ko NIMASA ko NNPC, miliyan uku kawai ake ware musu. Wadannan fa hukumomi ne da suke ta’ammali da tiriliyoyin kudade, kuma ku ce ba za a iya saye su ba? Gaskiya kawai yaudarar kanmu muke yi.
“Matukar aka ce hukumar da kake sanya wa ayyukanta idanu ita ce za ta rika daukar nauyinka, to tabbas batun sa’ido ya babu shi ma.
“Samar da wadatattun kudade ga ’yan majalisa domin ayyukan sanya idanu ne kawai zai tabbatar da ana aikata gaskiya kuma ana yin abubuwan da suka dace a bangaren kwamitocin majalisar,” in ji Farfesa Sulaiman.
A nasa bangaren, shugaban tawagar wakilan, Jide Oyekunle, ya yaba wa shugaban cibiyar, kan yadda ya ce yana aiki tukuru musamman wajen ba ’yan jarida horo a bangaren ayyukansu.