Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya yi kira ga ’yan jam’iyyar adawa da su zo a hada kai da gwamnatinsa don kara dora jihar a turbar ci gaba.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis, jim kadan bayan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta mika masa takardar shaidar cin zabe, karo na biyu.
- PDP ta kori wadanda suka dakatar da Ayu a Binuwai
- PDP ta janye dakatarwar da ta yi wa Shema, Anyim da Fayose
An ba shi shaidar ce tare da Mataimakinsa, Manasseh Daniel Jatau da ’ƴan majalisan dokokin jihar a ranar 18 ga watan Maris.
“Ina kira ga duk wadanda suka tsaya takara a zaben da ya gabata da su zo mu hada kai wajen ba da shawarwari na gari don ciyar da jihar mu gaba,” in ji Gwamnan.
Ya kuma kara tabbatar wa al’ummar Jihar Gombe cewa takardar shaida da ya karba shaida ce ta nuna cewa zai kara kwazo da himma dan karasa ayyukan da ya faro da kuma aza tubalin wasu sababbi.
Ya yaba wa hukumar INEC kan yadda ta bullo da sabbin dabaru a kokarinta na inganta harkokin zabe a Najeriya.
A jawabinsa na maraba, Kwamishinan hukumar zaben a Jihar Gombe Alhaji Umar Ibrahim, ya bukaci wadanda suka yi nasarar da su dauki nasarar tasu a matsayin amanar da masu zabe suka dora musu don ganin jihar da al’umma sun shaida ribar mulkin Dimokuradiyya.