✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku sa ido sosai kan ayyukan bata-gari a lokacin hunturu

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta ja hankalin jama’ar jihar su rika sanya idanu a kan bata-gari a lokacin hunturu. Kakakin rundunar, DSP Abdullahi…

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta ja hankalin jamaar jihar su rika sanya idanu a kan bata-gari a lokacin hunturu.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya yi kiran a madadin Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Babu Sani.

Ya jaddada bukatar a rika lura a wannan lokacin da hunturu ke shigowa saboda bata-gari kan yi amfani da damar su yi barna a gidaje a lokacin da masu su ke lullube a gida.

DSP Kiyawa, ya yi kira da jama’a su kiyayi kunna wuta barkatai, saboda lokacin sanyi lokaci ne da gobara ke saurin tashi.