Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta ja hankalin jama’ar jihar su rika sanya idanu a kan bata-gari a lokacin hunturu.
Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya yi kiran a madadin Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Babu Sani.
- Matsalar tsaro ba ta damu manyan Arewa ba —#SecureNorth
- KAROTA za ta dauki karin ma’aikata
- FCE Gombe za ta koma karatu ranar 9 ga Nuwamba
Ya jaddada bukatar a rika lura a wannan lokacin da hunturu ke shigowa saboda bata-gari kan yi amfani da damar su yi barna a gidaje a lokacin da masu su ke lullube a gida.
DSP Kiyawa, ya yi kira da jama’a su kiyayi kunna wuta barkatai, saboda lokacin sanyi lokaci ne da gobara ke saurin tashi.