✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ku ji tsoron Allah a alkawuranku — Lugga ga ’yan takarar gwamnan Kastina 

Wazirin Katsina, Farfesa Sani Abubakar Lugga, ya shawarci ’yan takaranr gwamnan jihar su ji tsoron Allah a alkawuransu na yakin neman zabe

Wazirin Katsina na biyar, Farfesa Sani Abubakar Lugga, ya shawarci ’yan takaranr gwamnan jihar su ji tsoron Allah a alkawuran da za su dauka na yakin neman zabe.

Farfesa Lugga ya yi kiran ne a matsayin shugaban taron Zauren Al’umma da kamfanin Media Trust, masu jaridun Aminiya da Trust TV, tare da hadin guiwar wadansu kafafen yada labarai suka shirya wa ’yan takarar gwamnan jihar a Katsina.

Ya yi jawabin ne a yayin bude taron da ke gudana a dakin taro na Hukumar Kula da Kananan Hukumomi ta Jihar Katsina a safiyar Asabar.

Haka zalika, Farfesan ya shawarci masu zabe da su ji tsoron Allah su yi abin da suke ganin har ga Allah shi ne daidai a lokacin zaben.

Sannan ya shawarci hukumar zabe da kuma jami’an tsaro da suma su sanya tsoron Allah wajen gudanar da ayyukansu a lokacin zaben don ganin cewa an dora kasa a turba madaidaiciya.