✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku guji zuwa ci-rani waje ta varauniyar hanya —ACIED Africa

Babban Daraktan ACIEDA Africa, Adeshile Adenekan ya bukaci su rika bin matakai da hanyoyin da suka kamata su mallaki takardun bulaguro da sauran abubuwan da…

Cibiyar Kasuwanci da Kirkira ta Afirka (ACIED Africa) ta roki ’yan Nijeriya musamman mata da ’yan mata, su guji zuwa ci-rani kasashen waje ba bisa ka’ida ba, domin su ne suka fi fadawa a hannun masu fataucin dan Adam.

Babban Daraktan ACIEDA Africa, Adeshile Adenekan ya bukaci su rika bin matakai da hanyoyin da suka kamata su mallaki takardun bulaguro da sauran abubuwan da suka dace don zuwa ci-rani cikin mutunci da aminci.

Adeshile Adenekan ya bayyana damuwar cibiyar kan ayyukan masu safarar mata da ’yan mata zuwa kasashen waje ba bisa ka’ida ba, da kuma yadda suka mayar da hankalinsu kan ’yan mata.

Ya ce, “Hadarin ya hada da yiwuwar a daure su a kurkuku ko a sayar da su domin yin karuwanci ko a yi musu fyade ko a kashe su a hanya, ko kuma a koro su daga kasashen da suka je saboda rashin takardu.

“Masu son zuwa aiki a wasu kasashe da yawa sukan makale a hanya ko su shiga mawuyacin hali da cin zali, ko a sayar da su a matsayin bayi don aikin karfi ko karuwanci ko su mutu a wuraren da ake tsare da su.

“Don haka, ya wajaba a hana fataucin ’yan mata, kuma iyaye mata su ba da gudunmawa wajen wayar da kansu game da hadarin zuwa ci-rani kasashen waje ta barauniyar hanya.”