Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta kalubalnaci shugabannin kabilar Ibo da su shawo kan masu neman ballewa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya domin kauce wa sake afkawa cikin wani yaki a kasar.
Dattawan sun jadadda cewa shirun da shugabannin kabilar ta Ibo suka yi a yayin da ake karkashe ’yan Arewa a yankinsu ba shi ne abu mafi a’ala ba.
- Gwamnati ta umarci kafafen yada labaran Najeriya su rufe shafukansu na Twitter
- Kano Pillars ta koma saman teburin Firimiyar Najeriya
Kakakin NEF, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya ce shugabannin Arewa sun yanke shawarar katse hanzarin barkewar duk wani yaki a Najeriya.
Sai dai ya ce rashin cewa uffan da shugabannin Ibon suka yi kan batun ya nuna cewa suna goyon bayan yunkurin ballewar.
Dattawan Arewan sun bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a Abuja bayan wata ganawar sirri da suka yi a ranar Litinin.