✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kowanne dan Najeriya yanzu yana da hannun jari a NNPC – Mele Kyari

Ya ce sam gwamnati ba ta sayar da kamfanin ba

Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, ya ce yanzu kowanne dan Najeriya na da hannun jari a kamfanin, kuma ya zama mallakin ’yan kasa.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunwarsa da gidan talabijin na Arise ranar Alhamis, lokacin da yake karin haske kan ko an cefanar da kamfanin ne.

A ranar Talata ce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon tambarin kamfanin da ke alamta cewa yanzu ya koma na kasuwanci.

Hakan a cewar Gwamnatin Tarayya ya sauya fasalin NNPC daga kasancewarsa mallakinta gaba daya zuwa cikakken kamfanin kasuwanci.

Lamarin dai ya jawo zazzafar muhawara a Najeriya, inda mutane da dama ke cewa an sayar da shi ne kawai ga ’yan kasuwa.

To sai dai a cewar Mele Kyari, ba sauya fasalin kamfanin suka yi ba, kawai dai sun yi wa tsarin tafiyar da hada-hadar shi kwaskwarima ne.

“NNPC mallakin ’yan Najeriya sama da miliyan 200 ne. Mu ne masu hannun jari a cikinsa, kuma kodayaushe masu hannun jarin na da wakilci a hanyoyin tafiyar da shi.

“Saboda haka, yanzu yana karkashin Ma’aikatar Man Fetur da Ma’aikatar Kudi, a madadin sauran bangarorin gwamnati, a madadin dukkanmu ’yan kasa ke nan.

“Tarayyar Najeriya ta kunshi jihohi da kananan hukumomi, hakan kuma na nufin ’yan Najeriya sama da miliyan 200.

“Amma ba zai yiwu dukkanmu mu zama masu gudanarwa a kamfanin ba. Kudurin Dokar Man Fetur na Kasa ya yi bayani karara cewa Shugaban Kasa ne zai nada Hukumar Gudanarwar kamfanin wacce za ta wakilici sauran ’yan kasa

“Saboda haka, harka ce ta wakilci ba wani boyayyen abu da wasu ke tunani ba,” inji Shugaban na NNPC.