✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kowa ya yi da kyau

Barka da warhaka Manyan Gobe Da fatan an yi Sallah lafiya. Ina fatan ba ku ci nama mai yawa ba. A yau na kawo muku…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Da fatan an yi Sallah lafiya. Ina fatan ba ku ci nama mai yawa ba.
A yau na kawo muku labarin ‘Kowa ya yi da kyau’.  Labarin na kunshe ne da yadda Ado ya sanya Audu ya zama yaron kirki.
A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

Kowa ya yi da kyau

A wata makaranata an yi wani yaro mai hazaka da karatu da ake kira Ado. A kullum shi yake yin na daya a ajinsu. Ga shi da ladabi da biyayya ga malamansa da iyayensa da kuma ‘yan ajinsa.
Akwai wani yaro a ajinsu Ado, sunansa Audu. Audu kazami ne kuma jakin a aji ne, akwai shi da rashin kunya ga malamai da kuma dukan daliban da ya fi karfi. Ya tsani Ado saboda yadda yake da hazaka bugu da kari duka malamai da dalibai suna sonsa.
Rannan mahaifin Ado ya yi masa kyautar alkalamin rubutu, da Audu ya gani sai ya tambayi Ado “a ina ka samu?” Ado ya ce “mahaifina ne ya ba ni.”
Da aka fita tara, sai Audu ya sace alkalamin a jakar Ado. Bayan an dawo, sai Ado ya duba amma bai ga alkalaminsa ba, sai ya kai kara wurin malaminsu. Malami ya sa aka bincika jakar kowa. A haka aka gano Audu ne ya sace alkalamin. Sai malamin ya ce zai dauki babban mataki a kan abin da Audu ya yi wa Ado. Amma da yake Ado mai yafiya ne sai ya ba maamin nasu hakuri,  inda kuma aka yi wa Audu afuwa. Audu ya yi mamakin irin wannan halin Ado. Tun daga ranar sai ya yi nadama, ya kuma zama dan kirki.
Da fatan Manyan Gobe za ku dauki darasi daga wannan labarin. Ku kasance kamar Ado; idan mutum ya sa cuce ku, to  kada ku rama, ku ma saka masa da alheri domin gyara halinsa.