✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun tafi-da-gidanka za ta fara hukunta kazamai a Oyo

Gwamnan Jihar Oyo Mista Seyi Makinde ya bada sanarwar bullo da shirin tsabtace muhalli a kananan hukumomi 33 da yankunan raya karkara 35 na jihar.…

Gwamnan Jihar Oyo Mista Seyi Makinde ya bada sanarwar bullo da shirin tsabtace muhalli a kananan hukumomi 33 da yankunan raya karkara 35 na jihar.

Gwamna Seyi Makinde ya kuma ce gwamnatinsa ta samar da kotunan tafi-da- gidanka da za su rika yanke hukuncin dauri da tara ga masu tara shara a cikin gidaje da kasuwanni da tashoshin mota da kan hanyoyi ba tare da kwashe ta ba.

Gwamna Makinde  yakuma  umarci dukkan wadanda ke zaune a gabar Kogin Ogunpa da ya ratsa sassan birnin Ibadan su kaurace wa wurin don guje wa ambaliyar ruwa.

Kwamishinan Tsabtace Muhalli na Jihar, Mista Kehinde Ayoola da Babban Sakataren Ma’aikatarsa, Dokta Bashiru Olanrewaju ne suka wakilci Gwamna Makinde, wajen ziyarar wasu unguwannin birnin Ibadan inda suka isar da sakon Gwamnan ga jama’a kan muhimmancin tsabtace muhalli da illar watsa shara a cikin magudanun ruwa da take haifar da kazanta da cututtuka masu yaduwa a tsakanin al’umma.

Da yake isar da sakon Gwamnan lokacin da ya ziyarci fadar Sarkin Hausawan Ibadan da sashen masu sana’ar fawa da ’yan Acaba da matsugunin mabarata a Unguwar Sabo Ibadan,  Babban Sakataren Ma’akatar Tsabtace Muhalli Dokta Bashiru Olanrewaju wanda ya jagoranci ayarinsa wajen kwashe shara daga magudanun ruwa da bola tare da raba jakar leda ta zuba shara ga jama’a, ya umarci jama’a su rika amfani da ledar wajen tara shara a ciki da kebe ta daga kusantar jama’a zuwa lokacin da kamfanonin kwasar shara za su kwashe a motocinsu.

Dokta Olanrewaju ya ce, gwamnatin ta bullo da sabon tsarin sayen sharar ledojin fiya-wata da kwalaben roba da murafen kwalaben lemun da makamantansu daga hannun mutane. Saboda haka ya shawarci jama’a su daina zubar da irin wannan shara a kan hanya da magudanun ruwa domin sun zama kudi a Jihar Oyo.

Sai dai ya ce daga yanzu duba-gari za su fara shiga cikin gidaje da wuraren taruwar jama’a domin tabbatar da ganin dokar tsabtace muhalli tana yin aiki. Ya ce, duk wanda aka samu da taka dokar zai dandana kudarsa ta hanyar yanke masa hukuncin tara ko dauri a gidan yari.

Ma’aikatar Tsaftace Muhallin ta gudanar da yekuwar ce da hadin gwiwar Hadaddiyar Kungiyar Gyara Unguwar Sabo a karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Alhaji Danjuma Garba Garas, wanda ya jagoranci mambobin kungiyar wajen gudanar da wannan muhimmin aiki.