✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Musulunci ta tsare mawaki ‘Mai Dubun Isa’ a gidan yari

An gurfanar da Mai Dubun Isa bisa zargin cin mutuncin Sheikh Tijjani Usman Zangon Bare-Bari, a TikTok, zargin da mawakin ya musanta

Kotun Musulunci a Jihar Kano ta tsare fitaccen mawakin Musulunci, Usman Mai Dubun Isa a gidan yari, bisa zargin cin mutuncin daya daga cikin jagororin darikar Tijjaniyya a jihar, Sheikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari.

An gurfanar da Mai Dubun Isa ne bisa zargin furta kalaman cin mutunci ga Sheikh Usman Zangon Bare-Bari, ta shafinsa na TikTok, wanda hakan ya sa malamin daukar matakin shari’a.

Sai dai a lokacin da aka gurfanar da Mai Dubun Isa a gaban kotun Musulunci da ke zamanta a PRP Gama a ranar Litinin, ya musanta zargin da ake masa.

Lauyan mawakin, A. J. Usman, ya bukaci a ba da belinsa, amma lauyan mai kara ya bayyana cewa yin hakan na iya zama hadari ga rayuwarsa, domin mabiyan malamin na iya far masa.

A kan haka ne alkalin kotun, Malam Nura Yusuf Ahmad, ya ba da umarnin a tsare Mai Dubun Isa a gidan yari, ya kuma dage sauraron shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Agusta mai kamawa.