Hakan kuwa na zuwa ne bayan alkalan kotun sun karbi jawabin Jihar Abiya, bayan lauyan ministan, Tijani Gazalli (SAN), ya amince kotun ta karbi bukatar Gwamnatin Jihar Abiya a matsayin mai kara ta 12 a sharia’ar.
Bayan nan ne Antoni-Janar na Jihar Legsa, Moyosore Onigbanjo (SAN), ya kalubalanci takwaransa na tarayya wanda ya ce bai kamata ba a matsayinsa na mai halartar zaman kotu ya rika saba umarninta.
Don haka ya mika bukatar shigar da kara tuhumar Malami da raina umarnin kotu.
Wannan kuwa na zuwa ne jim kadan bayan dawowa daga hutun takaitaccen lokaci a ranar Laraba.
Tun da farko, jagoran alklali bakwai na kotun, Mai Shari’a Inyang Okoro ya ce ya zama bangarorin da ke shari’ar su bi duk hukuncin da kotun ta yanke a shari’ar.
A nata bangaren, Mai Shari’a Amina Augie ta ce, “Kuna iya shigar da sabon kara bayan wannan.”
Alkalan kotun sun ce ya zama dole su cimma matsaya kan shari’ar sauyin kudin a yau.
Ya kuma bayyana cewa daga yanzu kotun ba za ta kara karbar bukatar duk wanda ya zo yana neman shiga bagarorin shari’ar ba.