✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta tsawaita lokacin amfani da tsoffin kudi

Za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.

Kotun Koli ta ta ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira da aka sauya wa fasali har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.

Kwamitin alkalai bakwai da suka yi zama kan batun a ranar Juma’a sun yi ittifakin cewa sauya fasalin kudin ya saba doka, saboda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin ne ba tare da tattaunawa da bangarorin gwamnati da suka kamata ba.

Jagoran alkalan Kotun Kolin, Mai Shari’a Inyang Okoro, ya bayyana cewa rashin tattauna batun tare da gwamnatocin jihohi da Majalisar Zartarwa ta Kasa da kuma Majalisar Koli ta Kasa ya mayar da sauyin kudin haramtacce.

Sun kara da cewa an fara aiwatar da dokar sauyin kudin ba tare da an bayar da isasshen lokaci ba, wanda hakan ya saba ba Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN).

Hukuncin Kotun Kolin da Mai Shari’a Emmanuel Agim ya karanta ta yi watsi da hujjar da Gwamnatin Tarayya ta bayar cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar da gwamnonin jihohi 16 suka shigar gabanta na kalubalantar dokar sauyin kudin.