✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta tabbatar wa tsagin Ganduje shugabancin APC na Kano

Kotun ta yi fatali da karar da Ganduje ya shigar.

Kotun Koli ta tabbatar wa da tsagin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano shugabancin jam’iyyar APC na jihar.

Wannan na zuwa ne bayan daukaka kara da tsagin tsohon Gwamnan Jihar, Ibrahim Shekarau ya yi na neman ta ayyana Haruna Danzago a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar.

Kwamitin Alkalai na kotun mai mambobi guda biyar, karkashin jagorancin Alkali Inyang Okoro ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a.

A cewar Mai shari’a Okoro, Kotun Daukaka Karar da ta saurari karar da gabarta mata da farko ba ta da hurumin yin haka, don haka karar ta zama abar korewa.

Haka nan, Kotun Kolin ta ce hukuncin da ta yanke ya shafi sauran kararraki biyun da aka daukaka a shari’ar.

Idan dai za a iya tunawa, Kotun Daukaka Kara ta kori kararraki ukun da aka gabatar mata a Fabrairun da ya gabata saboda rashin cika sharudda wajen shigar da kararrakin, tare da cewa matsalar ce ta cikin gida ce wadda ba sai an fita waje don magance ta ba.