Kotun Koli ta soke Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar kujerar Gwamnan Jihar Taraba a Jam’iyyar APC.
A ranar Laraba lauyoyi biyar na Kotun Kolin, karkashin jagorancin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun suke soke dan takarar.
- Barazanar kisa: Kotu ta sa a cafke shugaban APC na Kano
- Mata Musulmi sun nemi Majalisa ta gaggauta kafa dokar sa hijabi a makarantu
Gabanin haka, sai da Babbar Kotun Tarayya ta kori Sanata Bwacha bayan karar da David Sabo Kente, wanda ya nemi tsayawa takarar gwamna a Jam’iyyar APC ya sigar a watan Satumban 2022.
Kotun Kolin ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayyar bisa hujjar cewa haramtacce ne zaben dan takarar Gwamnan Taraba da APC ba ta gudanar, wanda ya samar da Bwacha.