✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun koli ta dage sauraren karar zaben Zamfara

Kotun kolin Najeriya ta dage karar da aka shigar gabanta zuwa ranar 9 ga watan Maris 2020, na zaben Gwamnan jihar Zamfara da aka yi.…

Kotun kolin Najeriya ta dage karar da aka shigar gabanta zuwa ranar 9 ga watan Maris 2020, na zaben Gwamnan jihar Zamfara da aka yi.

Alkalin alkalan Najriya Mai shari’a Tanko Muhammad, ne ya jagoranci mambobin mutum biyar, sannan ya bada umarnin dage karar zaben sakamakon rashin gabatar da cikakkun hujjoji da alkalin APC Robert Clark (SAN)  bai gabatarwa kotun ba, kan kalubalantar hukuncin kotun.

Mambobin jam’iyyar APC na jihar tare da tsohon Gwamnan jihar Abdulaziz Yari, ne suka bukaci kotun da sake duba hukuncin kotun da aka yanke na ranar 25 ga Mayu 2019,  inda suka bayyana kuri’un jam’iyyar APC a matsayin asarar kada kuri’a.

Jim kadan, da sanar da hukncin kotun aka sanar da jam’iyyar PDP a matsayin wanda ta lashe zaben jihar.