✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Kano ta umarci magidanci ya yanka zakaransa

Makwabcin mai zakaran ne ya kai kara saboda yana samunsa da cara

Wata kotun majistare da ke Gidan Murtala a Jihar Kano ta umarci wani mutum, Isyaku Shu’aibu, mazaunin unguwar Ja’en a birnin na Kano da ya yanka zakaransa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Halima Wali, ce ta yanke hukunci yayin zaman kotun na ranar Talata.

Tun da farko Makwabcin Isyaku mai suna Malam Yusuf Muhammad Ja’en ne ya shigar da karar a gaban kotun cewa zakaran yana shiga hakkinsa, inda yake hana shi barci da yawan cara.

Lokacin da aka karantowa wanda ake kara takardar karar, ya ce gaskiya ne zakaran na yawan yin cara kuma zai yanka shi ne a bikin “Good Friday” don haka ya roki kotun da ta sahale masa zuwa ranar.

Alkalin kotun ta amince da rokon nasa inda ta umarce shi da ya killace zakaran .

Sannan ta kuma umarce shi da ya yanka shi a ranar Jumu’a mai zuwa wato ranar “Good Friday” din.