Babbar Kotun jihar Jigawa da ke zamanta a Birnin Kudu, ta yanke wa wasu mutum hudu da ta samu da laifin aikata fyade ga kananan yara hukuncin daurin rai da rai.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Musa Ubale ne ya yanke hukuncin a ranar Talata.
Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Umar Danladi da Abdussalam Sale da Auwalu Yunusa da kuma Mu’azu Abdurrahman, bayan ta tabbatar da zarge-zargen da aka yi musu.
An yanke musu hukuncin ne daidai da tanade-tanaden sashe na 283 na kundin Penal Code ba jihar Jigawa na shekarar 2012 (wanda aka yi wa kwaskwarima).
Umar Danladi dai mazaunin Sabuwar Gwaram ne a karamar hukumar Gwaram, wanda ya yaudari wata karamar yarinya mai shekara takwas da take dawowa daga makaranta ya yi mata fyaden.
Shi kuwa Abdussalam Sake, mazaunin kauyen Rafawa a karamar hukumar Dutse, ya yi wa wata yarinya mai shekara 12 ne fyade, wacce ke kan hanyarta daga sabon garin Barnawa zuwa Kishin Gishin Gawa, inda ya aiketa, daga bisani kuma ya yi mata fyaden.
A masa bangaren kuwa, Auwalu Yunusu na kauyen Kafin Fulani a karamar hukumar Gwaram, ya yi wa ’yar shekara shida fyaden ne bayan ta dawo daga aiken da ya yi mata.
Na karshen kuwa, Mu’azu Abdulrahman daga garin Sabuwar Gwaram a karamar hukumar Gwaram an same shi ne da laifin yi wa ’yar shekara takwas fyade lokacin da take kan hanyarta ta dawowa daga makaranta.
Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Musa Ubale, ya ce kotun ta gamsu da shaidu da hujjojin da lauyan masu shigar da kara, Yahaya Abdullahi ya gabatar wa kotun.
Ya ce kotun ta yanke musu hukuncin ne daidai da tanadin dokokin jihar.