✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da zaben Lalong

Kotun Daukaka Kara da ke Jos a Jihar Filato, ta tabbatar da zaben Gwamnan Jihar Simon Lalong da kuma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed,…

Kotun Daukaka Kara da ke Jos a Jihar Filato, ta tabbatar da zaben Gwamnan Jihar Simon Lalong da kuma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed, bayan ta tabbatar da hukuncin da kotunan sauraron kararrakin zabe na Filato da Bauchi suka yi. Kotun ta yi watsi da karar da dan takarar kujerar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar PDP Sanata Jeremiah Useni da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed A. Abdullahi suka shigar a gabanta, saboda rashin kawo gamsassun shaidu.

Kotun ta ce Gwamna Lalong ya cancanci ya tsaya takarar Gwamnan Jihar a zaben da ya gabata, domin ya gabatar wa hukumar zabe takardar shaidar rubuta jarrabawar gama makarantar sakandare, da ya  samu a 1980.

Kotun ta yi bayanin cewa lauyan mai karar, bai iya kawo wa kotun cikakkiyar shaidar cewa Gwamna Lalong bai yi wa Hukumar INEC, cikakken bayanin kansa ba, a   wajen cike takardar tsayawa takarar.

Har ila yau kotun ta ce mai karar bai gamsar da kotun da cikakkiyar shada cewa an yi magudi a lokacin zaben ba. Don haka kotun ta yi watsi da karar, tare da tabbatar da hukuncin da kotun farko wadda ta yi watsi da karar.

Jagoran lauyoyin Jam’iyyar PDP Barista Edward Pwajok ya ce wanda suke karewa da Jam’iyyar PDP, ba su gamsu da hukuncin kotun  ba, don haka za su tafi Kotun Koli, don ganin an yi musu adalci.

Jagoran lauyoyin  APC da Gwamna Lalong, Garba Pwul (SAN) ya ce  a shirye suke su tafi Kotun Kolin domin sun yi imanin cewa hukuncin da Kotun Kolin za ta yanke, ba zai taba saba abin da kotunan baya suka yanke ba.