Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta ce nan da mako biyu masu zuwa za ta sanar da lokacin da za ta bayyana hukuncin da ta yanke kan kwace kujerar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP.
Kotun da ke zamanta a Abuja ta sanar da hakan ne bayan da ta kammala sauraron sauraron lauyoyin bangarorin da ke shari’ar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai gabanta kan kwace kujerarsa da Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta yi.
- Zaben Adamawa: An kasa gurfanar da Hudu Yunusa-Ari a kotu
- Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Yusuf Datti na NNPP
Gwamna Abba ya garzaya kotu nen yana kalubalantar hukuncin da kotun farko da ta soke 165,663 daga cikin kuri’u 1,019,602 da ya samu a zaben a matsayin ba halastattu ba, saboda rashin kwanan wata da hatimin INEC a jikin takardun kuri’un.
Soke kuri’un na Abba da alkalan suka yi ne ya sa Gawuna, wanda ya zo na biu a zaben da kuri’u 890,705 ya yi masa fintinkau.
Don haka a hukuncin na ranar 20 ga watan Satumba, karamar kotun ta bayyana babban abokin hammayarsa, Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC, a matsayin wada ya yi nasara.
Tun a lokacin Abba ya bayyana hukuncin a matsayin “rashin adalci” da kuma yi wa “tsarin shari’a dibar karan mahaukaciya,” da wannan sabon abu da ta kawo.
A yayin zaman kotun daukaka kara na ranar Litinin, babban lauyan Gwamna Abba, Wole Olanipekun (SAN), ya bukaci ta soke hukuncin karamar kotun, saboda a cewarsa, abin da ta yi wani kirkira ne da ya ci karo da hukunce-hukuncen da a baya kotun daukaka kara da Kotun Kolin suka yanke.
Amma a martaninsa, Babban lauyan APC Akin Olujimi, ya mayar da martani da cewa Kotunan Daukaka Kara sun yanke hukunci karara cewa rashin rattaba hannu a kan takardun kuri’un da aka kada daidai yake da magudin zabe kuma dokar
INEC sun fayyace ayyukan baturen zabe a rumfar zabe, ciki har da tabbatar da sa hannu da kwanan wata a bayan kowacce kuri’a.
Wadanda Abba da NNPP suke kara su ne Gawuna, APC da kuma Hukumar Zabe da Kasa (INEC), wadda kotun sauraron kararrakin zaben ta umarta da janye shaidar cin zaben Abba ta ba wa Nasiru Yusuf Gawuna.