✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Ƙoli ta tabbatar wa Farouk Lawan ɗaurin shekaru biyar

Tirka-tirkar dai ta faro ne tun bayan da tsohon ɗan Majalisar Wakilan ya nemi cin hancin $3m.

Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin zaman gidan dan Kande na shekaru biyar da aka yanke wa tsohon ɗan Majalisar Wakilai Farouk Lawan.

Kotun ta tabbatar da samun Farouk Lawan da laifin karɓar cin hanci na kuɗi dala 500,000 daga hannun fittaccen dan kasuwar nan, Femi Otedola wanda shi ne shugaban kamfanin Zenon Petroleum and Gas Limited.

Ƙarar da aka ɗaukaka ta buƙaci a soke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yanke a ranar 24 ga Fabrairu, 2022, inda ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari tare da wanke shi a kan tuhume-tuhume biyu daga cikin ukun da aka gurfanar da shi a kai, waɗanda suka shafi cin hanci da rashawa.

A hukuncin da mai shari’a John Okoro ya shirya amma mai shari’a Tijjani Abubakar ya karanta, Kotun Ƙolin ta ce ƙarar da Farouk Lawan ya shigar ba ta da cancantar da za a saurare ta sannan ya yi watsi da ita.

Tawagar masu yanke hukuncin da ta ƙunshi alƙalai biyar gaba ɗaya sun tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke tsohon dan majalisar tun a shekarar 2022.

Ana iya tuna cewa tun a shekarar 2013 aka soma gurfanar da Farouk Lawan kan zargin karɓar na goro a lokacin da yake Shugaban Kwamitin Tallafin Man Fetur na Majalisar Wakilai.

A wancan lokacin dai, an gurfanar da Farouk Lawan kan zargin neman cin hancin Dala miliyan uku daga hannun Femi Otedola domin wanke kamfaninsa daga cikin wadanda ake zargi da badaƙalar kuɗin tallafin man fetur.