✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu za ta karɓi shaidar wakilin Aminiya a shari’ar garkuwa da mutane

Wata Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zama a yankin Dogarawa na Ƙaramar Hukumar Zariya, na shirin karɓar shaidar ɗaya daga cikin wakilan Aminiya a…

Wata Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zama a yankin Dogarawa na Ƙaramar Hukumar Zariya, na shirin karɓar shaidar ɗaya daga cikin wakilan Aminiya a shari’ar da take yi kan zargin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Kotun dai ta amince wakilin Aminiya ya gabatar da shaidar wani hoton bidiyo da ya naɗa yayin da waɗansu mutum biyu da ake zargi da ta’adar garkuwa da mutane ke shan titsiye a hannun ’yan sanda bayan shigarsu hannu.

Tun a zaman kotun da ya gabata ne lauyan da ke gabatar da ƙara, Dari Bayero, ya kafa hujjar cewa yana da shaidar wani hoton bidiyo da yake neman kotun ta ba shi damar gabatar mata.

Kotun wadda ta amince da wannan buƙatar ta nemi a gabatar mata da hoton bidiyon da kuma wakilin Aminiya da ya naɗi bidiyon a yayin gudanar da aikinsa.

Kazalika, Alƙalin kotun, Mai Shari’a Abdulkadir Sabo Mahmud, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 17 ga watan Janairu a yayin da lauyan waɗanda ake ƙara, Nura Tukur bai ƙalubalanci buƙatar ba.

Ana iya tuna cewa, ana tuhumar wasu mutum biyu — Idris Mustapha wanda aka fi sani da Idi Maizomo da Isah Ibrahim— da laifuka biyu da suka shafai garkuwa da mutane.

Aminiya ta ruwaito cewa ana tuhumar mutanen biyu da garkuwa da wasu mutum huɗu — Ibrahim Yakubu da Yusha’u Sani da Abdallah Mohammed Awwal ɗan shekara biyar da Aisha Mohammed Awwal ’yar kimanin shekaru biyu da rabi — mazauna unguwar Nagoyi da ke Zariya tun a ranar 28 ga watan Janairun 2021.

Ana kuma tuhumar ababen zargin biyu da neman kuɗin fansa na Naira miliyan 14 a matsayin sharaɗin sakin waɗanda suka yi garkuwa da su.

Waɗannan laifuka dai sun ci karo da tanadin sassa na 247(1) da kuma na 246(c) da ke Kundin Dokokin Laifuka na Jihar Kaduna.