✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa Mataimakin Shugaban Kenya

An janye tuhumar kan badakalar dalar Amurka miliyan 60.

An janye tuhumar da ake yi wa Mataimakin Shugaban Kenya, Rigathi Gachagua ta badakalar dalar Amurka miliyan 60.

Wata kotu a kasar ce ta amince da bukatar da masu gabatar da kara suka shigar na janye karar saboda rashin isassun shaidu.

A watan Yulin da ya gabata aka tuhumi Gachagua tare da wasu mutum tara da aikata rashawa, zargin da ya ce shi bai aikata ba.

Yayin zaman kotun a ranar Alhamis, Alkali Victor Wakumile, ya ce kotun ta amince da bukatar da masu gabatar da kara suka shigar ta neman janye karar da aka shigar a kan Gachagua.

Sai dai Alkalin ya gargadi wadanda ake zargin kan cewa akwai yiwuwar nan gaba a sake kama su a gurfanar da su.

A farkon wannan wata ne jami’i mai gabatar da kara, Noordin Haji, ya nemi kotun ta janye karar almundahanar da aka shigar a kan Gachagua saboda rashin hujjoji.

Kawo yanzu, masu gabatar da kara sun janye kararraki da dama karkashin sabuwar gwamnatin Shugaban Kasar, William Ruto.