An janye tuhumar da ake yi wa Mataimakin Shugaban Kenya, Rigathi Gachagua ta badakalar dalar Amurka miliyan 60.
Wata kotu a kasar ce ta amince da bukatar da masu gabatar da kara suka shigar na janye karar saboda rashin isassun shaidu.
- Mawaki 50 Cent zai shirya fim kan Hushpuppi
- Na sanar da Sarki Charles III ba ni da gidan kaina a Birtaniya —Buhari
A watan Yulin da ya gabata aka tuhumi Gachagua tare da wasu mutum tara da aikata rashawa, zargin da ya ce shi bai aikata ba.
Yayin zaman kotun a ranar Alhamis, Alkali Victor Wakumile, ya ce kotun ta amince da bukatar da masu gabatar da kara suka shigar ta neman janye karar da aka shigar a kan Gachagua.
Sai dai Alkalin ya gargadi wadanda ake zargin kan cewa akwai yiwuwar nan gaba a sake kama su a gurfanar da su.
A farkon wannan wata ne jami’i mai gabatar da kara, Noordin Haji, ya nemi kotun ta janye karar almundahanar da aka shigar a kan Gachagua saboda rashin hujjoji.
Kawo yanzu, masu gabatar da kara sun janye kararraki da dama karkashin sabuwar gwamnatin Shugaban Kasar, William Ruto.