Wata Kotun Shari’ar Musulinci a Jihar Kano, ta yanke wa wani mai suna Murtala Adamu hukuncin dauri na watanni shida saboda aikata badala.
An dai kama Murtala Adamu tare da fitacciyar jarumar nan ta TikTok, Murja Ibrahim Kunya.
Kotun wadda ke zamanta da unguwar Gama da ke Karamar Hukumar Kumbotso ta kuma bai wa matashin zabin biyan tarar naira dubu talatin ( 30.000) bisa samunsu da laifin tayar da haniya da aikata badala.
Mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala, ya shaida wa kotun cewa an kama Murtala Adamu tare da Murja a unguwar Hotoro, bayan jami’an Hukumar Hisbah sun kai samame kan korafin da mazaunar unguwar suka shigar.
Abidin Murtala ya bayyana cewa laifukan da ake tuhumar Murtala Adamu sun saba da sashe na 275 na kundin dokokin final-kot.
Dangane da hakan ne Alkalin Kotun, Mai Shari’a Nura Yusuf Ahmed, ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida ko zabin biyan tarar Naira dubu talatin.
Kazalika, kotun ta yanke alakarsa da Murja Kunya da cewa ba shi ba ita, sannan ta haramta masa zuwa unguwar tsawon shekaru biyu, kuma muddin aka gan shi zai dandana kudarsa.
Aminiya ta ruwaito cewa, an kuma ba wai Murtala Adamu takardar kulla yarjejeniya wadda ya cike kuma ya sanya hannu.