Kotu ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ba tare da zabin biyan tara ba ga wani magidanci da ya yi wa ’yar cikinsa mai shekara 15 fyade har ta dauki ciki.
Kotun da ke zamata a Jihar Legas ta yanke wa mutumin hukuncin ne bayan gamsuwarta da hujjojin da masu shigar ta kara suka gabatar mata a kan wanda ake zargin.
Alkalin Kotun, Mai Shari’a Abiola Soladoye, ya ce: “Wannan abin a la’anta ne, saboda haka an yanke wa wanda ake zargin hukuncin daurin rai-da-rai ba tare da zabin biyan tara ba.”
Tun da farko, mai gabatar a kara ya shaida wa kotun cewa magidancin ya yi wa ’yar cikin tasa fyade har ta dauki ciki ne a tsakanin watan Disamban shekarar 2018 zuwa watan Yunin 2019 a gidansa da ke Unguwar Agege a Jihar Legas.
’Yar tasa ta ce dubun mahaifin nata ta cika ne bayan ta sanar da wani jami’in jinkai a makarantarsu da abin da mahaifin nata yake aikatawa.
Alkalin ya ce, “Abin da wanda ake zargin ya aikata ya kazanta, abin Allah wadai ne sannan ba abin a yi wa afuwa ba ne bisa tanadin sashe ne 137 na Dokar Hukunta Manyan Laifuka ta Jihar Legas ta 2015.
“Wannan abin assha na saduwa da ’yar cikinsa ya kai matuka wajen muni da zama abin kunya da kuma saba wa dabi’ar mutum mai lafiyayyen tunani.
“Saboda haka an yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai ba tare da zabin biyan tara ba,” inji alkalin.