Babban Kotun Jihar Legas da ke zamanta a Ikeja, ta yanke wa kasurgumin mai garkuwa da mutanen nan, Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans hukuncin daurin rai da rai.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Hakeem Oshodi ne ya yanke hukuncin ranar Juma’a.
- Matsalar tsaro: Dalilin da muka tuhumi Waziri kan kalamansa – Masarautar Katsina
- Harin Rasha: Shi ne mafi girma tun bayan Yakin Duniya na II
Kazalika, kotun ta kuma yanke wa wasu mutum biyu hukunci, bayan ta same su da hannu a sace wani hamshakin dan kasuwa, Donatus Duru.
Alkalin dai ya samu Evans da sauran mutanen da laifuka biyun da aka tuhume su da aikatawa masu jibi da yin garkuwa da Mista Donatus, wanda shi ne Manajan Daraktan kamfanin harhada magunguna na Maydon.
Sauran wadanda aka yanke wa hukuncin tare da Evans din sun hada da Uche Amadi da Okwuchukwu Nwachukwu.
Alkalin ya ce masu shigar da kara sun gamsar da kotun kan hujjojinsu game da zarge-zargen da aka yi wa mutanen, musamman faya-fayan bidiyon da suka gabatar a gaban kotun.
Sai dai alkalin ya kuma wanke tare da bayar da umarnin sakin wani mai suna Ogechi Uchechukwu da wasu tsofaffin sojoji biyu; Chilaka Ifeanyi da Victor Aduba, saboda rashin bayar da cikakkun hujjojin da ke nuna suna da hannu a aikata laifin.