Wata kotun yankin Incheon a Koriya ta Kudu ta yanke wa wata mata hukuncin daurin rai-da-rai saboda kama da hannu a mutuwar mijinta.
Bayanan da kotun ta samu sun nuna matar da saurayinta ne suka yi sanadiyar mutuwar mijin nata a wani rafi a 2019, don su samu damar mallake inshora ta miliyan 800 a kudin kasar ($563,976) da yake da ita.
- NNPC da Daewoo Group sun kulla yarjejeniyar gyaran matatar mai ta Kaduna
- ’Yan kasuwar da za a cefanar wa filayen jiragen saman Najeriya
An ce Lee Eun-hae tare da saurayinta, Cho Hyun-soo, sun ja marigayin zuwa rafi a yankin Gapyeong, alhali bai iya ninkaya ba, wanda hakan ya yi sanadiyar ruwa ya tafi da shi.
Bincike ya nuna kafin jan marigayin zuwa rafi, masu laifin sun taba yunkurin hallaka shi amma ba su yi nasara ba.
Yayin da aka yanke wa matar daurin rai-da-rai, shi kuwa saurayin zaman kurkuku na shekara 30 kotu ta yanke masa.