✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai saboda aikata fyade

Ya hada baki da karti suka dauke wata yarinya da karfi suka yi mata fyade a wani kango.

Wata Babbar Kotun Jihar Ekiti da ke zamanta a birnin Ado-Ekiti ta yanke wa wani matashi mai kimanin shekaru 27, Farotimi Samuel hukuncin daurin rai da rai saboda aikata fyade.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Adekunle Adeleye ya ce kotun ta dauki matakin ne bayan gamsuwa da hujjojin da masu kara suka gabatar a gabanta.

“Mun tabbatar da laifin nasa kamar yadda aka zarge shi, don haka mun yanke masa hukuncin daurin rai da rai.”

Takardar tuhumar matashin dai ta nuna cewa an aikata laifin ne ranar 29 ga watan Janairun 2018, a unguwar Oke-Ureje ta birnin Ado-Ekiti.

Takardar ta ci gaba da cewa wanda ake zargin ya hada baki da wasu inda suka yi wa wata yarinya ’yar shekara 14 fyade.

Ita ma da take bayar da shaida a gaban kotun, yarinyar ta ce ta je sayo garin kwaki da sukari ne lokacin da wasu karata uku suka tare ta a hanya.

“Sun rufe min baki sannan suka kai ni cikin wani kango inda dukkansu suka yi lalata da ni. Ko da na gan su babu wanda zan gane daga cikinsu,” inji yarinyar.