✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci matar da aka saki ta mayarwa da mijinta firiji

Wata kotun Sharia Court ll, da ke unguwar Magajin Gari, a jihar Kaduna a yau Talata ta umarci wacce suka rabu da mijinta mai suna…

Wata kotun Sharia Court ll, da ke unguwar Magajin Gari, a jihar Kaduna a yau Talata ta umarci wacce suka rabu da mijinta mai suna Umma Zakariyya ta mayarwa da tsohon mijinta mai suna Muhammad Muntari kayan da suka hada da: firiji, tukunyar gas ta girki da sauran kwanukan ajiye abinci.

A yayin zaman kotun Mai shari’a Murtala Nasir, ya ce kotun ta bayar da wannan umarnin a maida wa Muhammad, kayansa bayan ya shigar da karar bukatar kayansa.

Duk da yake Muhammad Muntari, bai gabatar wa da kotun shaidu cewa, kayan mallakinsa ne ba, amma Alkalin kotun ya bukace shi da ya rantse da Alkur’ani, sannan kuma ya aikata hakan.