✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci a saki zakaran kwallon tennis na duniya, Novak Djokovic

An dai tsare shi ne saboda karya dokar COVID-19.

Wani alkalin kotu a kasar Australia ya umarci a saki zakaran kwallon tennis din nan na duniya, Novak Djokovic, daga hannun jami’an tsaro sannan a bashi takardar izinin shige da ficen da aka kwace masa.

A ranar Litinin ne Mai Shari’a Anthony Kelly ya ba da umarnin sakin nasa a cikin miti 30 sannan a dawo masa da dukkan takardun da aka kwace daga hannunsa.

Hakan dai ya dawo wa dan wasan damar da yake da ita ta yiwuwar fafatawa a gasar Grand Slam karo na 21 da ke tafe a kasar Australia.

Sai dai lauyoyin gwamnatin kasar sun shaida wa kotun cewa Ministan Shige da Fice na da damar jinkirta hukuncin zuwa wani lokaci, wanda hakan ke nufin dan wasan na iya rasa bude gasar wacce za a bude ranar 17 ga watan Janairu.

Gwamnatin ta Australia dai ta kwace izinin shiga kasar ta Djokovic, jim kadan da isarsa birnin Melbourne ranar Laraba domin bikin bude gasar, saboda karya dokar da ta tanadi dukkan wanda ba dan kasar ba dole ne a yi masa rigakafin COVID-19.

Dan wasan, wanda shaida ta nuna ba a yi masa rigakafin ba, ya ce ba ya bukatar rigakafin tun da dai yana da shaidar da ke nuna ba ya dauke da cutar.

Tun lokacin dai da aka soke izinin shigar tasa kasar, Djokovic ya kasance a killace a cikin otal da ke birnin Melbourne.

Sai dai yanzu babu tabbacin inda dan wasan ya shiga lokacin da aka fara zaman kotun, saboda ba a gan shi ba lokacin da aka fara shari’ar ta ranar Litinin.

Lauyoyinsa dai sun mika korafe-korafe 11 da suka daukaka kara kan soke takardar izinin shiga kasar, inda suka bayyana matakin a matsayin wanda ba shi da wani tushe ballantana makama.