Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata ta umarci a ci gaba da tsare tsohon Shugaban Kwamitin yi wa Harkar Fansho ta Kasa Garambawul (PRTT), Abdulrashid Maina a kurkuku.
Umarnin ya biyo bayan kin amincewa da bukatar lauyoyinsa ta neman bayar da belinsa.
- Janyewar Amurka: Ina makomar Afghanistan bayan kama mulkin Taliban?
- Matsalar taro: An rufe manyan hanyoyi da kasuwannin wasu sassan Jihar Katsina
Alkalin kotun, Mai Shari’a Ahmed Mohammed ne dai ya ki amincewa da bukatar wacce lauyan Mainan, David Iorhemba ya shigar bisa cewa ba ta cika ka’ida ba.
Lauyan masu shigar da kara (EFCC), Andrewa Ocholi ya soki lamirin bukatar, inda ya ce tuni ya shigar da wata bukatar a gaban kotu da ke neman a ayyana Maina a matsayin wanda bai cancanci a sake bayar da shi beli ba a nan gaba.
Da yake yanke hukunci, alkalin ya ce kotun ba ita ya kamata ta saurari bukatar bayar da belin ba.
Daga nan ne ya umarci a koma gaban kotun Mai Shari’a Okon Abang, wanda a baya dama shi yake sauraron karar domin ya duba bukatar bayar da Mainan beli.
Ana dai tuhumar Abdulrashid Maina tare da kamfaninsa mai suna Common Input Property and Investment Ltd da zarge-zargen laifuka har guda 12 da suke da jibi da almundahanar kudaden da yawansu ya kai kusan Naira biliyan daya.
An dai fara gurfanar da shi ne a gaban kotu ranar 25 ga watan Oktoban 2019, inda daga bisani Mai Shari’a Abang ya ba da umarnin garkame shi a gidan yarin Kuje, har zuwa lokacin da aka saurari bukatar belinsa.
Sai dai bayan bayar da belin nasa, Maina ya cika wandonsa da iska ya kuma ki dawowa, in ban da daga bisani da aka kamo shi a Jamhuriyar Nijar.
Alkalin dai ya ce la’akari da haka, Maina bai cancanci a sake bayar da shi beli a karo na biyu ba.
Daga nan ne ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa hudu ga watan Oktoba mai zuwa. (NAN)