Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin tsare Sanata Ali Ndume a gidan yarin da ke Kuje.
Mai Shari’a Okon Abang ya ba da umarnin tsare Sanata Ndume ne saboda tsohon Shugaban Kwamitin Yi wa Harkar Fansho na Kasa Garanbawul, Abdulrasheed Maina, ya ki bayyana a gaban kotun.
- ‘Najeriya na cikin kasashe 12 mafiya hadari ga rayuwar yara’
- Limami da mutum 17 ne ’yan bindiga suka sace a Zamfara —’Yan sanda
- Matsin tattalin arziki na dan lokaci ne —Ministar Kudi
Sanata Ndume Mai Wakiltar Borno ta Kudu shine dai ya karbi belin Maina wanda ake zargi da karkatar da kudaden fansho na biliyoyin Naira.
Kotun ta ce dan Majalisar ya gaza bayar da kwakkwarar hujjar da za ta hana ta kwace Naira miliyan 500 da ya ajiye a lokacin ya karbi belin Maina a ranar 5 ga watan Mayu, 2020.
Alkalin kotun ya ce za a tsare dan majalisar a gidan yarin ne har sai an kammala cike-ciken hannanta wa Gwamanti Tarayya kudaden.
A ranar 18 ga watan Nuwamba kotun ta janye belin da ta bayar na Maina ta kuma umarci hukumomin tsaro su kamo shi a duk inda suka gan shi su kawo shi ta yanke masa hukunci kan tsallake belin da ya yi.
A lokacin, Mai Shari’a Abang ya ba wa Sanata Ndume zuwa ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba ya bayyana dalilin da zai hana kwace kudin da ya ajiye a lokacin da aka ba shi beli Maina.
A watan Oktoba, Ndume ya shaida wa kotun cewa ba da son ransa ya karbi belin Maina ba duk da cewa dan mazabar da yake wakilta ne.
Ndume ya ce ya karbi belin ne saboda matar Maina da iyayensa sun yi masa magiya saboda kotu ta shardanta masa kawo dan Majalisar Dattawa ya tsaya masa.
A watan Oktoban 2019 ne hukumar EFCC ta gurfanar da Maina, bisa zargi 12 masu alaka da ta’ammuli da haramtattun kudade daga 2011 zuwa 2014.