✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare matasa masu garkuwa da mutane

Kotun Majistare ta 16 da ke Nomansland a Kano ta bayar da umarnin a tsare wadansu matasa 23 bisa zarginsu da yin garkuwa da mutane…

Kotun Majistare ta 16 da ke Nomansland a Kano ta bayar da umarnin a tsare wadansu matasa 23 bisa zarginsu da yin garkuwa da mutane a garin Kiru da ke Jihar Kano.

Mai gabatar da kara, Sufeto John Edward ya shaida wa kotun cewa a watan Yulin da ya gabata wani mai suna Kabiru Salisu mazaunin Kiru ya hada baki da wadansu abokan barnarsa da suka hada da Shu’aibu Idris da Sani Musa da Bawa Adamu da Magaji Sule da Danladi Isyaku da Isa Abubakar da Aliyu Isma’il da sauransu, inda suka dauki miyagun makamai kamar su bindiga da adda da sanduna suka auka a gidan wani mutum da ke garin Kiru sakamakon haka suka kama tare da yin garkuwa da wadansu daga cikin iyalan gidan da suka hada da Muttaka da Aliyu da Hasiya da Maryam Sa’idu, sannan kuma suka nemi kudin fansa daga iyayensu.

Sai dai dukan wadanda ake zargin sun musanta laifuffukan da ake tuhumarsu da su na hadin baki da fashi da makami da mallakar makamai ba tare da izni ba da kuma garkuwa da mutane, laifuffukan da suka saba wa sashe na 6 (a) (b) LNF wanda aka yi wa gyara a shekarar 2001 da  sashe na 273 na Kundin Shari’a na Final Kod.

Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Khalil Mahmud ya bayar da umarnin a tsare wadanda ake zargi a gidan kurkuku zuwa ranar 15 ga watan Nuwamban bana.