✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tabbatar wa da Gwamna Nasir El-Rufai kujerarsa 

Kotun saurarar kararrakin Zabe a Kaduna ta tabbatarwa da Gwamnar Jihar Nasir El-Rufai kujerarsa a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna da aka yi a…

Kotun saurarar kararrakin Zabe a Kaduna ta tabbatarwa da Gwamnar Jihar Nasir El-Rufai kujerarsa a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna da aka yi a watan Maris 2019.

Alkalin Kotun Ibrahim Bako, wanda ya yanke hukuncin hakan a yau Litinin ya yi watsi da karar da dan takarar PDP Isa Ashiru, ya shigar a saboda rashin kwararrun shaidu.

Da yake bayani ga manema labarai a harabar Kotun a Kaduna, Lauyan Gwamna El-Rufai, Babban Lauya Abdulhakeem Mustapha, ya ce katun ta gamsu da cewa mai kara bashi da shaidan da zai nuna cewa Nasir El-Rufai bai ci zabe ba.

Ya ce, kotu ta gamsu da cewa masu karar sun bata mata lokaci ne saboda rashin shaidu wanda hakan yasa aka yi watsi da karar tare da bayyana Gwamna Nasir El-Rufai a matsayin wanda ya lashe zaben.

Shima da yake tattaunawa da manema labarai Shugaban Jamiyar PDP a jihar Felix Hassan Hyet, ya bayyana rashin jindadin sa ga hukuncin na Kotun inda ya ce, jami’iyarsu zata fitar da matsayinta akan wannan hukunci nan bada dadewa ba, bayan  sun tattauna da lauyoyinta da kuma dan takararsu.

Ya kuma nemi magoya bayansu da su kara hakuri su kuma saurari matsayin jam’iyar ta su nan bada dadewa ba.‎