✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tabbatar da Sanwo-Olu a matsayin halastaccen Gwamnan Legas

Kotun ta yanke hukuncin cewa korafin jam’iyyar PDP da dan takarar Olajide Adediran ba shi da tushe,

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Legas ta tabbatar da nasarar Babajide Sanwo-Olu a matsayin halastaccen gwamna.

Wannan na kunshe ne cikin wani hukunci da ilahirin alkalan suka amince da shi, kuma Mai shari’a Mikail Abdullahi ya karanta a madadin alkalan uku ranar Litinin.

Kotun ta yanke hukuncin cewa korafin jam’iyyar PDP da dan takarar Olajide Adediran ba shi da tushe, don haka kuma sun yi watsi da karar.

A kokarin tabbatar da hukuncin da ta yanke, kotun da farko ta nanata kin amincewar farko-farko da bangarorin da ke cikin shari’ar suka nuna kafin ta yi nazari game da batutuwan da ta bijiro da su don yin shari’a.

Kotun ta saurari bahasi a kan tambayar ko tana da hurumin sauraron karar, inda mai shari’a Mika’il Abdullahi ya ce tabbas kotun tana da hurumi.

Sai kuma batu na biyu da ke neman hukunci a kan ko jam’iyyar APC ta ba da sunan Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat bisa hanyar da ta dace su tsaya mata takara a zaben 18 ga watan Maris.

Kotun ta kafa hujjoji da tanade-tanaden tsarin mulki da kuma na kundin zabe da dumbin shari’o’in da aka yanke hukunci dangane da batun, inda ta jaddada cewa korafin batu ne da ya kamata a ce tuni an kammala da shi kafin gudanar da zabe kuma ba shi da alaka da zabukan da aka kalubalanta.

Kotun ta kuma ce masu korafin ba ’ya’yan jam’iyyar APC ba ne wadda ake kara ta hudu don haka ba su da hurumin kalubalantar zaben fid-da-gwanin da ya fito da ’yan takarar biyu.