Kotun sauraron kararrakin zabe ta Jihar Zamfara da ke zamanta a Sakkwato ta tabbatar da zaben Dauda Lawal Dare a matsayin gwamnan jihar.
Kwamitin alkalan ya ce koken da jam’iyyar APC ta shigar bai cancanta.
- Tinubu ya isa New York don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya
- An daure mai unguwa a Kano kan zargin satar ƙofofi
Shugabar kwamitin, Mai shari’a Cordelia Ogadi wadda ta jagoranci wasu mambobi biyu ta kara da cewa, masu shigar da karar sun kasa tabbatar da hujjojinsu kan zaben.
Alkalin ta ce wadanda suka shigar da karar sun gaza warware hujojjinsu ta hannunsu shaidunsu.
Shaidun wadanda ke kara sun bayyana cewa an samu tashin hankali a lokacin da ake gudanar da zabe a Maradun, kuma sun gabatar da dalilai da hujjojinsu a fili, inda suka ce jami’an tsaro sun ba da umarnin daukar wani mataki kan ayyukan.
Alkalin ta kara da cewa mai gabatar da kara na uku, wadda ita ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kuma ba da shaida kan yadda gudanar da zabe har zuwa lokacin bayyana sakamako.
Don haka ta yi watsi da karar saboda rashin cancanta da kuma gaza tabbatar da kura-kuran da ake zargin an tafka yayin zaben, inda ta ci tarar masu shigar da kara Naira 500,000.