Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Kano ta soke dakatarwar da aka yi wa ‘yan majalisar dokokin jihar biyar wadanda suka ki goyon bayan tube tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
A ranar 15 ga watan Maris ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da ‘yan majalisar bisa zarginsu da dauke sandar majalisar a lokacin zaman sauraron bincike da kuma sauke tsohon Sarkin.
Alkalin kotun Mai Shari’a Alagoa ya ce dakatarwar ba ta bisa ka’ida kuma ta saba wa kundin mulkin kasa.
Don haka ya bada umarnin a biya ‘yan majalisun hakkokinsu da suka hadar da albashinsu da kudin alawus-alwaus nasu na tsawon lokacin da aka dakatar da su.
- Kurar da ta tashi bayan tube Sarki Sanusi II
- Kotu ta bada umarnin a saki Sanusi II
- Da umarnin Buhari aka tube Sarki Sanusi II – Kwankwaso
‘Yan majalisu biyar da lamarin ya shafa su ne wadanda suka ki goyon bayan cire tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a ranar 16 ga watan Maris, lamarin da ya janyo hayaniya a zauren majalisar.
‘Yan majalisar da lamarin ya shafa sun hadar da Garba Yau Gwarmai mai wakilta mazabar Kunchi/Tsanyawa, da Labaran Abdul Madari da ke wakiltar mazabar Warawa, sai Isyaku Ali Danja mai wakiltar mazabar Gezawa, da Mohammed Bello da ke wakiltar mazabun Rimingado da Tofa, sai Salisu Ahmed Gwangwazo mai wakiltar mazabar Kano Municipal.