Kotu a birnin New York ta saki tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump ba tare da gindaya wasu sharudda ba a shari’ar da aka fara dangane da zarge-zarge masu alaka da biyan makuden kudade gabanin zaben 2016.
Trump dai ya musanta dukkanin tuhume-tuhume 34 da ake masa, yayin zaman shari’ar a ranar Talata karkashin jagorancin Mai Shari’a Juan Merchan wanda ke matsayin karon farko a tarihin Amurka da wani tsohon shugaba ko mai ci ya taba gurfana gaban kotu.
- Donald Trump ya musanta dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa
- Dan jaridar da aka kora saboda caccakar Gwamnan Borno ya sami aiki a Turkiyya
Alkalin da ya jagoranci shari’ar Juan Merchan, ya dage lokacin ci gaba da sauraren shari’ar har zuwa watan Janairun 2024, ko da ya ke lauyoyin Trump sun bukaci dawo da lokacin kusa, lura da yadda lokacin shari’ar ya yi daidai da lokacin zaben fid-da-gwani don tunkarar zaben shugaban kasa na 2024, zaben da Trump ke shirin sake tsayawa takara.
Cikin tuhume-tuhume 34 da ake yi wa Trump dai har da biyan makuden kudade ga mutane daban-daban wadanda ake ganin su suka kai shi ga nasara a zaben 2016, ciki har da jarumar fina-finan badala da ya yi mu’amala da ita da kuma wani da ke da bayanin yadda tsohon shugaban ke da wani da da ya haifa ba tare da aure ba.
Sauran tuhume-tuhumen da Trump ya musanta sun hada da tayar da hankali tare da tunzura magoya bayansa bayan faduwa a zaben 2019, wanda ya kai ga rikicin Capitol da ya yi sanadin mutuwar mutum shida.
Sai dai a jawabinsa ga magoya bayansa a wata fadarsa da ke birnin Florida, Trump mai shekara 76, ya bayyana tuhumar a matsayin cin mutunci ga Amurka baki daya.
Ya bayyana cewa laifi daya da ya san ya aikata ba tare da tsoro ba shi ne bayar da kariya ga Amurka daga masu yunkurin rusa ta.