Babbar Kotun Jihar Kaduna ta sake dage zaman sauraron shari’ar shugaban kungiyar ’yan shi’a ta IMN, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, Zeenatu zuwa ranar 31 ga watan Maris.
Kotun yayin zamanta na yau Litinin, ta dage sauraron shari’ar domin bai wa bangaren masu shigar da kara damar kammala gabatar da korafe-korafensu.
- Hukumar NDLEA ta yi wawan kamu, ta tono hodar iblis a gidan wani basarake
- Mutum miliyan 2.5 sun yi rajistar jam’iyyar APC a Kano – Ganduje
- Shugaban Jamhuriyar Nijar ya lashe Kyautar Shugabancin Afirka
Jagoran masu shigar da kara kuma babban sakataren Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna, Chris Umar ne ya tabbatar da hakan jim kadan bayan zaman sauraron shari’ar da aka kwashe sama da awanni ana gudanarwa.
Umar ya ce kawo yanzu masu karar sun gabatar wa da kotun shaidu akalla 14 sannan kuma da kayayyakin da za su tsaya a matsayin madogarar hujjojin nasu, sai dai bai ambaci kayayyakin ba.
Shi kuwa lauyan wadanda ake tuhuma, Femi Falana (SAN), ya shaida wa manema labarai cewa daga cikin kayayyakin da aka gabatar wa kotun akwai rikodin sautin murya da na bidiyo, bindigogi, layukan waya da makamantansu.
Falana ya ce bangarensa na lauyoyi masu kare wadanda ake tuhuma, za su fara gabatar da hujjojinsu yayin zaman kotun na gaba, inda masu kara za su kammala gabatar da korafe-korafensu.