Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bai wa Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA damar ci gaba da tsare Mataimakin Kwamishinan Dan Sandan da aka dakatara, DCP Abba Kyari bayan ta kama shi kan zargin safarar hodar ibilis.
Mai Shari’a Zainab Dimka Abubakar ce ta ba da umarnin bayan wata bukata da hukumar ta shigar da zimmar neman ci gaba da tsare DCP Kyari da wasu mutum shida tsawon mako biyu.
- Mun bai wa gwamnati da ASUU wa’adin mako daya su sulhunta —Kungiyar Dalibai
- Rikicin Ukraine: Farashin mai ya tashi a kasuwar duniya
Aminiya ta ruwaito cewa, Mai shari’a Dimka ta kuma dage zaman sauraron bukatar neman beli da Abba Kyarin ya gabatar ta bakin lauyarsa, Cynthia Ikena zuwa ranar Alhamis.
BBC ya ruwaito cewa wadanda za a ci gaba da tsarewar su ne: DCP Abba Kyari, ACP Sunday J. Ubia, ASP James Bawa, Sufeto Simon Agirigba, Sufeto John Nuhu; Chibunna Patrick Umeibe, Emeka Alfonsus Ezenwanne.
Sanarwar da NDLEA ta fitar a ranar Talata ta ce wanda ake zargi da safarar hodar iblis din na 6 da na 7 (Umeibe da Ezenwanne) sun amsa laifinsu cewa sun shigar da ita Najeriya ne daga Habasha.
Ta kara da cewa su kuma wadanda ake zargi na 1 zuwa na 5 (Kyari, Ubia, Bawa, Agirigba, Nuhu) ‘yan sanda ne da suka kama na 6 da na 7 kuma suka kai su NDLEA don yin bincike.
“Saboda binciken da NDLEA ta gudanar ya nuna cewa na 1 zuwa na 5 sun ci amanar aiki kuma sun shiga an dama da su wajen safarar miyagun kwayoyi da kuma saka hannu wajen lalata hujja a kan masu laifi ta mua’amala da koken,” a cewar sanarwar.