Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta umarci DPO din ofishin ’yan sanda da ke unguwar Kuntau a Jihar da wadansu ’yan sanda biyu su biya wani matashi diyyar Naira miliyan uku saboda cin zarafinsa wani matashin da suka yi.
Tun a watannin baya ne aka yi karar matashin ofishin ’yan sanda na Kuntau bisa sabanin da ya shiga tsakaninsa da wani matashi.
- An kashe hakimi da dansa a Kudancin Kaduna
- Fitila ta kona jariri kwana daya da haihuwarsa
- Na kashe mutum 10 —Dan kungiyar asiri
- Tsohon lakcaran KADPOLY ya harbi matarsa ya kashe kansa
Sai dai a wancan lokaci’yan sandan na Kuntau sun yi zargin cewa matashin ya yi musu rashin kunya musamman dan sanda mai binciken lamarin, Sufeto Abdullahi Daura, don haka suka dauki matakin ladabtar da shi inda suka masa duka.
Takardar karar ta ci gaba da cewa daga nan ’yan sandan suka lakada wa matashin dukan kawo Wuka.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Louis Allagoa ya bayar da umarnin cewa wadanda ake zargin su biya Naira miliyan uku na cin zarafinn matashin tare da neman afuwarsa a kafafen watsa labarai.